ABNA24 : Jaridar ta yi ishara da halin da ake ciki a kasar ta Amurka ta fadace-fadace a tsakanin magoya bayan muhimman yan takarar shugabancin kasar biyu Donald Trump da kuma Joe Baidan.
Ita kuwa tashar talabijin NBC ta ce; Maáikatar harkokin cikin gida ta bukaci jamiánta da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin kare manyan gine-ginen gwamnatin tarayya a cikin birnin Washington.
A cikin babban birnin kasar na Amurka an kafa wuraren bincike da kuma shinge-shinge na siminti musamma a kusa da fadar mulkin kasar ta “White House”
A cikin makwannin bayan nan dai an rika samun fadace-fadace a tsakanin magoya bayan ‘yan takarar shugabancin kasar Joe Baiden da kuma shugaba mai ci Donald Trump.
342/